Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hawan Fanisau


Gabatarwa

Hawan Fanisau shi ne cikamakon hawan da sarki yake yi a hawan Sallar Layya. Shi kuma ana yin sa a ranar huɗu ga salla.

Sarki yana hawa ya fita ta Ƙofar Ƙwaru, sannan ya shiga Soron Ɗinki, ta Makwarari, Kwanar Gabari, ‘Yan Mota, Bakin Zuwo, Ƙoƙi, sannan ya fita taƘofar Mazugal. Sai ya tasa Arewa ya bi titinIBBta gabanKasuwa Ujile, ta gaban filin Dalar Gayaɗa ya tsallaka mararrabar titin Katsina da Kasuwar Sansannin Alhazai. Ya gangara ta sansanin sojojin sama. Idan ya je ƙarshen shingen sansanin sai ya karyaka hagu ya shiga ɗoɗar har zuwa Fanisau.

Yanzu sarki ya iso Fanisau, tun fitowar sarki daga gida akwai wasu hakimai a gabansa wasu kuma a bayansa kamar yadda ake yi a hawan Ɗorayi. Hakiman gabansa za su ɓurtane da sukuwa su kai ƙofar gidan sarki na Fanisau su tsaya. Idan sarki ya zo gab da gidan a filin ƙofar gida sai ya ja ya dakata har sai sauran hakiman baya sun shige shi sun je sun yi jere da su da waɗanda suka rigaye su dama da hagu sannan sarki ya sauka ya ratsa ta tsakiyarsu ya shiga gida. Sannan suma su sauka su tafi masauki.

Bayan sarki ya ɗan huta, sai ya fito fada haka nan ma hakimai da sauran masu sarauta. Idan aka yi gaisuwa aka tashi, sai kuma a yi sallar Azahar. Ana idar da salla sai mai ta fari ya harba, sai a fara shirye-shiryen hawa har zuwa sallar la’asar. Ana idar da sallar La’asar sai sarki ya hau. Sai gida.

Ana sake dawowa ta hanyar da aka bi har zuwa Ƙofar Mazugal. Idan sarki ya shige ta Gabas ya saka gabansa Yamma, sai ya miƙe ɗoɗar har zuwa mararrabar Kwanar Dala. sannan ya tasa Kudu ya shiga kwanar Dala, ya bi ta nesa kaɗan daDutsen Dala, har zuwa Kwanar dala. Daga nan sai ‘Yan gurasa, Bakin Zuwo, Tudun Wada, Tudun Nufawa, Kwanar Goda, Marmara, zuwa mararrabar Kasuwar Mandawari. Sai kuma ya juya Gabas zuwa mararrabar Gidan Shatima. A nan zai dakata bayan dama tun kafin zuwansa hakiman gabansa sun riga su je Ƙofar Ƙwaru da sukuwa, hakiman bayansa su zo su wuce shi da sukuwa. Bayan sun gama jeruwa hagu da dama, sai sarki ya ƙarasa ya sauka ya ratsa ta tsakiyar su suna gaisuwa ana karɓa. Idan sarki ya shiga gida sai sauran mahaya su sauka su tafi nasu gidajen sai kuma shekara idan Allah ya kai mu.

Manazarta:


Gwangwazo (2004). Gamzaki mai Asubahi, In Ya fito Gari Ya Waye, Sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub